7 Dukan amfanin gonakin da aka shuka a gaɓar Kogin Nilu za su bushe, iska ta fyauce su.
8 Duk wanda sana'arsa ta kama kifi ce a Kogin Nilu zai yi ƙugi ya yi kuka, gama ƙugiyoyinsa da tarunansa za su zama marasa amfani.
9 Waɗanda suke yin tufafin lilin za su fid da zuciya,
10 shugabanni da ma'aikata za su karai su kuma damu.
11 Shugabannin birnin Zowan wawaye ne! Mutanen Masar mafi hikima za su ba da gurguwar shawara! Ta ƙaƙa za su iya dosar sarki su faɗa masa, cewa su ne suka gāji masana da sarakuna na dā can?
12 Sarkin Masar, ina mashawartan nan naka masu hikima? Watakila za su iya faɗa maka shirye-shiryen da Ubangiji Mai Runduna ya yi domin Masar.
13 Shugabannin Zowan da na Memfis wawaye ne. Su ake zaton za su bi da al'ummar, amma sai suka bi da su a karkace.