16 Zai nutsar da jiragen ruwa mafi girma mafi kyau.
17 Girmankan ɗan adam zai ƙare, za a hallakar da fāriyar ɗan adam, Ubangiji ne kaɗai za a ɗaukaka sa'ad da wannan rana ta yi,
18 za a shafe gumaka ƙaƙaf.
19 Mutane za su ɓuya a kogwannin duwatsu, ko su haƙa ramummuka a ƙasa, suna ƙoƙarin tserewa daga fushin Ubangiji, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa, sa'ad da ya zo domin ya girgiza duniya.
20 Sa'ad da wannan rana ta yi za su zubar da gumakan da suka yi na zinariya da azurfa, za su bar wa ɓeraye da jemagu.
21 Sa'ad da Ubangiji ya zo domin ya girgiza duniya, jama'a za su ɓuya a cikin kogwannin tuddai da ramummukan duwatsu, suna ƙoƙari su ɓuya daga fushinsa, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa.
22 Kada ku dogara ga 'yan adam. Wace daraja take gare su?