12 Ubangiji Mai Runduna yana kiranku ku yi kuka, ku yi makoki, ku aske kawunanku, ku sa tsummoki.
13 A maimakon haka sai kuka yi dariya, kuka yi biki. Kuka yanka tumaki da shanu don ku ci, kuka sha ruwan inabi. Kuka ce, “Gara mu ci mu sha! Gobe za mu mutu.”
14 Ubangiji Mai Runduna ya ce mini, “Ko kusa ba za a gafarta musu wannan mugunta ba muddin ransu. Ni, Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
15 Ubangiji Mai Runduna ya faɗa mini in tafi wurin Shebna, mai hidimar iyalin gidan sarki, in ce masa,
16 “Kana tsammani kai wane ne? Wa ya ba ka 'yancin sassaƙa wa kanka kabari a jikin duwatsu?
17 Yana yiwuwa kai wani abu ne, amma Ubangiji zai ɗauke ka, ya jefar.
18 Zai dunƙule ka kamar ƙwallo ya jefa ka a cikin ƙasar da ta fi girma. A can za ka mutu a kusa da karusan da kake fāriya da su. Abin kunya kake a gidan maigidanka!