6 Saboda haka Allah ya aiko da la'ana ta hallaka duniya. Jama'arta suna karɓar sakayyar abin da suka aikata. 'Yan kalilan ne suka ragu da rai.
7 Kurangun inabi sun bushe, ruwan inabi ya yi kaɗan. Dukan wanda yake farin ciki a dā, yanzu sai baƙin ciki yake yi,
8 kaɗe-kaɗen garayunsu da gangunansu na farin ciki sun ƙare.
9 Babu sauran waƙar farin ciki ga mashayan ruwan inabi, ba kuma wanda zai ƙara jin daɗin ɗanɗanar ruwan inabi.
10 A cikin birni kome ya birkice, an kulle kowane gida don a hana mutane shiga.
11 Mutane za su tsaya a tituna, suna ihu, suna neman ruwan inabi. Farin ciki ya ƙare har abada, ya ƙare a ƙasar.
12 Birnin ya zama kango, an farfashe ƙofofinsa.