6 A kan Dutsen Sihiyona Ubangiji Mai Runduna zai shirya wa dukan sauran al'umman duniya biki da abinci irin na adaras da ruwan inabi mafi kyau.
7 A can ne zai kawar da baƙin cikin da ya lulluɓe dukan sauran al'umma.
8 Ubangiji zai hallaka mutuwa har abada! Zai share hawaye daga idanun kowane mutum, ya kawar da kunyar da jama'arsa suke sha a duniya duka. Ubangiji ne da kansa ya faɗa!
9 Sa'ad da wannan ya faru, kowa zai ce, “Shi Allahnmu ne! Mun dogara gare shi, ya kuwa cece mu. Shi ne Ubangiji. Mun dogara gare shi, yanzu kuwa muna da farin ciki domin ya cece mu!”
10 Ubangiji zai kiyaye Dutsen Sihiyona, amma za a tattake jama'ar Mowab a ƙasa, kamar yadda ake tattake tattaka cikin taki.
11 Za su miƙa hannuwansu kamar suna ƙoƙarin yin ninƙaya, amma girmankansu zai jā hannuwansu ƙasa a duk sa'ad da suka ɗaga.
12 Allah zai lalatar da kagaran Mowab da dogayen garukansu, ya rushe su ƙasa su zama ƙura.