1 Rana tana zuwa da jama'a za su raira wannan waƙa a ƙasar Yahuza.Birni ƙaƙƙarfa ne,Allah kansa yake tsare garukansa!
2 A buɗe ƙofofin birnin,A bar amintacciyar al'umma ta shiga,Al'ummar da jama'arta take aikata abin da yake daidai.
3 Kai kake ba da cikakkiyar salama, ya Ubangiji,Ga waɗanda suke riƙe da manufarsu da ƙarfi,Waɗanda suke dogara gare ka.
4 Ku dogara ga Ubangiji har abada.Zai kiyaye mu kullayaumin.
5 Ya ƙasƙantar da masu girmankai,Ya hallaka ƙaƙƙarfan birnin da suke zaune ciki,Ya rusa garunsa ƙasa.
6 Waɗanda aka zalunta, a kansa suke tafiya yanzu,Suna tattaka shi da ƙafafunsu.