6 Zai ba da ruhun adalci ga waɗanda suke alƙalai, ƙarfin hali kuma ga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofin birni.
7 Har da annabawa da firistoci, tangaɗi suke yi, mashaya ne. Sun sha ruwan inabi da barasa da yawa, suna ta tuntuɓe barkatai. Annabawan sun bugu ƙwarai, har ba su iya fahimtar wahayin da Allah ya aiko musu ba, firistoci su ma sun bugu, har sun kāsa yanke shari'un da aka kawo musu.
8 Duk sun cika teburorin da suke zaune da amai, ba inda ba su amaye ba.
9 Suna gunaguni a kaina suna cewa, “Su wa wannan mutum yake tsammani yana koya musu? Wa yake bukatar jawabinsa? Sai ga 'yan yaran da aka yaye kaɗai yake da amfani!
10 Yana ƙoƙari ya koya mana baƙaƙe baƙaƙe, da shaɗara shaɗara, da babi babi.”
11 Idan ba za ku saurare ni ba, to, Allah zai yi amfani da baƙi masu magana da harshen da ba ku sani ba, su koya muku darasi.
12 Ya miƙa muku hutawa da wartsakewa, amma kun ƙi saurarawa gare shi.