11 Amma mugaye sun shiga uku, za a sāka musu bisa ga abin da suka aikata.
12 Masu ba da rance da ruwa suna zaluntar jama'ata, masu ba da bashi kuwa suna cutarsu.Ya jama'ata, shugabanninku a karkace suke bi da ku, saboda haka ba ku san inda za ku nufa ba.
13 Ubangiji a shirye yake ya hurta maganarsa, a shirye yake ya hukunta al'ummai.
14 Ubangiji ya kawo dattawa da shugabannin jama'arsa a gaban shari'a. Ga laifin da ya same su da shi, “Kun washe gonakin inabi, kun cika gidajenku da abin da kuka ƙwato daga matalauta.
15 Ba ku da izinin da za ku ragargaza jama'ata, ku cuci matalauta, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
16 Ubangiji ya ce, “Duba irin girmankai da matan Urushalima suke da shi! Suna tafe suna hura hanci, a koyaushe suna ta fara'a irin ta yaudara, suna takawa ɗaya ɗaya a hankali da mundaye a ƙafafunsu, suna cas cas.
17 Amma zan hukunta su, in aske kawunansu, in bar su ƙwal.”