12 Ya amsa ya ce, “Kuna tsammani babban sarki ya aiko ni don in daɗa wa ku da sarki kurum dukan magana? Sam, ina magana ne da jama'ar da suke a kan garu, waɗanda za su ci kāshinsu su kuma sha fitsarinsu, kamar yadda ku kanku za ku yi.”
13 Sa'an nan ya tsaya ya ta da murya da harshen Ibrananci, ya ce, “Ku saurara ga abin da Sarkin Assuriya yake faɗa muku.
14 Yana muku kashedi, cewa kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku, Hezekiya ba zai iya cetonku ba.
15 Kada kuma ku bari ya rinjaye ku ku dogara ga Ubangiji, har ku sa tsammani Ubangiji zai cece ku, ya hana sojojinmu na Assuriya su cinye birninku.
16 Kada ku kasa kunne ga Hezekiya. Sarkin Assuriya yana umartarku ku fito daga cikin birni ku sallama. Za a yardar muku duka ku ci 'ya'yan inabi daga gonakinku, da 'ya'yan ɓaure na itatuwan ɓaurenku, ku kuma sha ruwa daga rijiyoyinku na kanku,
17 har babban sarki ya sāke zaunar da ku a wata ƙasa mai kama da taku, inda akwai gonakin inabi da za su ba da ruwan inabi, da hatsi don yin gurasa.
18 Kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku, da cewa Ubangiji zai kuɓutar da ku. Ko gumakan waɗansu al'ummai sun ceci ƙasashensu daga Sarkin Assuriya?