18 Dukanmu mun sani, ya Ubangiji, yadda sarakunan Assuriya suka hallakar da al'ummai masu yawa, suka mai da ƙasashensu kufai, marasa amfani,
19 suka ƙaƙƙone gumakansu waɗanda ba Allah ba ne ko kaɗan, siffofi ne kurum na itace da na dutse, da mutane suka yi da hannuwansu.
20 Yanzu dai, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga Assuriyawa domin dukan al'umman duniya su sani kai ne Allah kai kaɗai.”
21 Sa'an nan Ishaya ya aiki manzo zuwa wurin sarki Hezekiya, ya faɗa masa amsar Ubangiji a kan addu'ar sarki.
22 Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima yana yi maka dariya, kai Sennakerib, yana kuma yi maka ba'a.
23 Wa kake tsammani kana raina, kana yi masa ba'a? Ba ka ba ni girma ba, ni Allah mai tsarki na Isra'ila.
24 Ka aike da barorinka don su yi mini fāriya, da cewa ka ci nasara da duwatsu mafi tsayi da karusanka, har da ƙwanƙolin Dutsen Lebanon. Kana fāriya da cewa a can ka sare dogayen itatuwan al'ul da na fir, ka kuma kai wuri mafi nisa na jeji.