13 Dare farai na yi ta kuka saboda azaba,Sai ka ce zaki yake kakkarya ƙasusuwana.Na zaci Allah zai kashe ni.
14 Muryata ƙarama ce, ba kuma ƙarfi,Na kuwa yi kuka kamar kurciya,Idanuna sun gaji saboda duban sama.Ya Ubangiji, ka cece ni daga dukan wannan wahala.
15 Me zan iya faɗa? Ubangiji ne ya yi wannan.Ina da ɓacin zuciya, ba na iya barci.
16 Ya Ubangiji, zan bi ka, kai kaɗai.Ka warkar da ni, ka bar ni da rai.
17 Ɓacin zuciyata zai juya ya zama salama.Ka ceci raina daga dukan hatsari,Ka gafarta dukan zunubaina.
18 Ba wanda yake yabonka a lahira,Matattu ba za su iya dogara ga amincinka ba.
19 Masu rai ne suke yabonka,Kamar yadda nake yabonka yanzu.Iyaye za su faɗa wa 'ya'yansu irin amincinka.