17 Ɓacin zuciyata zai juya ya zama salama.Ka ceci raina daga dukan hatsari,Ka gafarta dukan zunubaina.
18 Ba wanda yake yabonka a lahira,Matattu ba za su iya dogara ga amincinka ba.
19 Masu rai ne suke yabonka,Kamar yadda nake yabonka yanzu.Iyaye za su faɗa wa 'ya'yansu irin amincinka.
20 Ya Ubangiji, ka riga ka warkar da ni!Za mu kaɗa garayu mu kuma raira waƙar yabo,Za mu raira yabo cikin Haikalinka muddin ranmu.
21 Haka ya faru bayan da Ishaya ya faɗa wa sarki ya sa curin da aka yi da 'ya'yan ɓaure a kan marurun, ya kuwa warke.
22 Sarki Hezekiya ya riga ya yi tambaya ya ce, “Me zai zama alama ta cewa zan iya zuwa Haikali?”