3 Duk wanda aka rage a Urushalima, wanda Ubangiji ya nufa da rayuwa, za a ce da shi mai tsarki.
4 Ta wurin ikonsa Ubangiji zai shara'anta al'ummar, ya kuma tsarkake ta, ya wanke laifin Urushalima, har da na jinin da aka zubar a can.
5 Sa'an nan a kan Dutsen Sihiyona, da a kan dukan waɗanda suka tattaru a can, Ubangiji zai aika da girgije da rana, hayaƙi da hasken harshen wuta kuma da dare. Darajar Ubangiji za ta rufe, ta kuma kiyaye birnin duka.
6 Ɗaukakarsa za ta inuwantar da birnin daga zafin rana, ta sa ya zama lafiyayyen wurin da aka kāre daga ruwan sama da hadiri.