17 Ya bi da manyan sojoji zuwa hallaka,Sojojin karusai da na dawakai.Sun faɗi warwar, ba za su ƙara tashi ba,An hure su kamar 'yar wutar fitila!
18 Amma Ubangiji ya ce,“Kada ku maƙale wa abubuwan da suka wuce,Ko ku riƙa tunanin abin da ya faru tuntuni.
19 Ku duba abin da nake shirin yi.Yana ta faruwa ma, kuna iya ganinsa yanzu!Zan yi hanya a cikin jeji,In kuma ba ku rafuffukan ruwa a can.
20 Har da namomin jeji za su girmama ni,Diloli da jiminai za su yi yabonaSa'ad da na sa kogunan ruwa su yi gudu a hamada,Domin su ba da ruwa ga zaɓaɓɓun mutanena.
21 Su ne mutanen da na yi domin kaina,Za su raira yabbaina!”
22 Ubangiji ya ce,“Amma ba ni kuka yi wa sujada ba,Kun gaji da ni, ya Isra'ila.
23 Ba ku kawo mini hadayun ƙonawa na tumaki ba,Ba ni kuke girmamawa da hadayunku ba.Ban nawaita muku da neman hadayu ba,Ko in gajiyar da ku da roƙon turare.