1 Ubangiji ya ce,“Babila, ki sauko daga kan gadon sarautarki,Ki zauna a ƙasa cikin ƙura.Dā ke budurwa ce, birnin da ba a yi nasara da shi ba!Amma ba sauran taushi da kuma rashin ƙarfi!Ke baiwa ce yanzu!
2 Ki juya dutsen niƙa, ki niƙa gari!Ki kware lulluɓi! Ki tuɓe kyawawan tufafinki!
3 Mutane za su gan ki a ƙasƙance, a kunyace kuma,A tuɓe ki tsirara kamar yarinyar da take baiwa.Zan ɗauki fansa, ba kuwa wanda zai hana ni.”
4 Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya fanshe mu,Sunansa Ubangiji Mai Runduna ne!