14 Amma mutanen Urushalima suka ce,“Ubangiji ya yashe mu!Ya manta da mu.”
15 Saboda haka Ubangiji ya amsa ya ce,“Mace za ta iya mantawa da jaririnta,Ta kuma ƙi ƙaunar ɗan da ta haifa?Ya yiwu mace ta manta da ɗanta,To, ni ba zan taɓa mantawa da ku ba.
16 Ya Urushalima, ba zan taɓa mantawa da ke ba,Na rubuta sunanki a gabana.
17 “Su waɗanda za su sāke gina ki suna tafe yanzu,Waɗanda suka lalatar da ke kuwa za su tashi.
18 Ki dudduba, ki ɗaga idonki, ki ga abin da yake faruwa!Mutanenki suna tattaruwa suna komowa gida!Hakika, da yake ni ne Allah Mai Rai,Za ki yi fāriya da mutanenki,Kamar yadda amarya take fāriya da kayan adonta!
19 “Aka lalatar da ƙasar, ta zama kufai,Amma yanzu za ta yi wa waɗanda suke komowa domin su zauna cikinta kaɗan.Waɗanda suka lalatar da ke kuwa,Za a kawar da su daga gare ki.
20 Mutanenki da aka haifa a lokacin zaman talala,Wata rana za su ce miki,‘Wannan ƙasa ta yi kaɗan ƙwarai,Muna bukatar ƙarin wurin zama!’