1 Ubangiji ya ce,“Duk mai jin ƙishi ya zo,Ga ruwa a nan!Ku da ba ku da kuɗi ku zo,Ku sayi hatsi ku ci!Ku zo ku sayi ruwan inabi da madara,Ba za ku biya kome ba!
2 Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba?Don me za ku ɓad da albashinku, amma kuna ta shan yunwa?Ku kasa kunne gare ni, ku yi abin da na faɗa,Za ku sha daɗin abinci mafi kyau duka.
3 “Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni,Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai!Zan yi tabbataccen alkawari da ku,Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.
4 Na sa ya zama shugaba, da shugaban yaƙi na al'ummai,Ta wurinsa kuwa na nuna musu girmana.
5 Yanzu kuwa za ku kira al'ummai, baƙi,Dā ba su kuwa san ku ba, ko da rana ɗaya,Amma yanzu za su sheƙo a guje domin su haɗa kai da ku!Ni, Ubangiji Allahnku, Allah Mai Tsarki na Isra'ila,Zan sa dukan wannan ya faru,Zan ba ku girma da daraja.”
6 Ku juyo wurin Ubangiji, ku yi addu'a gare shi,Yanzu da yake kusa.