18 Bisa ga ayyukansu, haka zai sāka musu hasala, a kan maƙiyansa kuwa ramawa, a kan abokan gābansa, zai rama, da kuma a kan ƙasashen da suke a bakin gāɓa.
19 Saboda haka waɗanda suke yamma za su ji tsoron sunan Ubangiji, waɗanda suke wajen gabas kuma za su ji tsoron ɗaukakarsa, gama zai zo kamar rafi mai tsananin gudu, wanda iskar Ubangiji take korawa.
20 Zai zo Sihiyona ya zama mai fansa ga waɗanda suke na Yakubu, su da suka juya suka bar mugunta.
21 Ubangiji ya ce, “Amma ni, wannan shi ne alkawarina da su, Ruhuna da yake tare da ku, da kalmomina da na sa a bakunanku, ba za su rabu da bakunanku ba, ko daga bakunan 'ya'yanku, ko na jikokinku, tun daga wannan lokaci har abada.”