1 A shekarar da sarki Azariya ya rasu na ga Ubangiji. Yana zaune a kursiyinsa a Sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika Haikali.
2 Kewaye da shi sai ga waɗansu talikai masu kama da harshen wuta a tsaye, ko wannensu yana da fikafikai shida. Ko wannensu ya rufe fuskarsa da fiffike biyu, jikinsa kuma da fiffike biyu, sauran fiffike biyu ɗin kuma, da su yake tashi.
3 Suna ta kiran junansu suna cewa,“Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki!Ubangiji Mai Runduna Mai Tsarki ne!Ɗaukakarsa ta cika duniya.”
4 Amon muryoyinsu ya sa harsashin ginin Haikali ya girgiɗa, Haikalin kansa kuma ya game da hayaƙi.
5 Sai na ce, “Sa zuciyata ya ƙare! Na shiga uku! Kowace maganar da ta fito bakina zunubi ce, ina zaune a tsakanin mutane waɗanda duk maganarsu zunubi ce, ba ta da tsarki. Amma yanzu da idona na ga Sarki, Ubangiji Mai Runduna!”
6 Sa'an nan ɗaya daga cikin talikan ya tashi ya sauko zuwa gare ni, yana riƙe da garwashin wuta wanda ya ɗauko da arautaki daga bagade.
7 Ya taɓa leɓunana da garwashin wutar ya ce, “Wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”