1 Ki tashi, ya Urushalima, ki haskaka kamar rana,Daukakar Ubangiji tana haskakawa a kanki kamar rana!
2 Duhu zai rufe sauran al'umma,Amma hasken Ubangiji zai haskaka a kanki,Daukakarsa za ta kasance tare da ke!
3 Za a jawo al'ummai zuwa ga haskenki,Sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki.
4 Ki duba kewaye da ke, ki ga abin da yake faruwa,Mutanenki suna ta tattaruwa domin su komo gida!'Ya'yanki maza za su taho daga nesa,Za a ɗauki 'ya'yanki mata kamar yara.
5 Za ki ga wannan, ki cika da farin ciki,Za ki yi rawar jiki saboda jin daɗi.Za a kawo miki dukiyar al'ummai,Wato waɗanda suke a ƙasashen hayi.