4 Ki duba kewaye da ke, ki ga abin da yake faruwa,Mutanenki suna ta tattaruwa domin su komo gida!'Ya'yanki maza za su taho daga nesa,Za a ɗauki 'ya'yanki mata kamar yara.
5 Za ki ga wannan, ki cika da farin ciki,Za ki yi rawar jiki saboda jin daɗi.Za a kawo miki dukiyar al'ummai,Wato waɗanda suke a ƙasashen hayi.
6 Babban ayarin raƙuma zai zo daga Madayana da Efa.Za su zo daga Sheba, su kawo zinariya da kayan ƙanshi.Mutane za su ba da labari mai daɗi a kan abin da Allah ya yi!
7 Dukan tumaki na Kedar da Nebayot,Za a kawo miki su hadaya,A kuwa miƙa su a kan bagade domin Ubangiji ya ji daɗi.Ubangiji zai darajanta Haikalinsa fiye da dā.
8 Waɗannan jiragen ruwa fa? Suna tafe kamar gizagizai,Kamar kurciyoyi suna komowa gida.
9 Jiragen ruwa ne suke zuwa daga manisantan ƙasashe,Suna kawo mutanen Allah gida.Suna tafe da azurfa da zinariya,Domin su girmama sunan Ubangiji,Allah Mai Tsarki na Isra'ila,Wanda ya sa dukan al'ummai su girmama mutanensa.
10 Ubangiji ya ce wa Urushalima,“Baƙi ne za su sāke gina garukanki,Sarakunansu kuma za su bauta miki.Na hukunta ki da fushina,Amma yanzu zan nuna miki alheri da jinƙai.