1 Don me ba za ka kware sararin sama, ka sauko ba? Duwatsu za su gan ka, su girgiza saboda tsoro!
2 Za su karkaɗu kamar ruwan da yake tafasa a wuta. Ka zo ka bayyana ikonka a kan abokan gābanka, ka sa al'ummai su yi rawar jiki a gabanka.
3 Ka taɓa zuwa ka yi abubuwan banrazana waɗanda ba mu sa tsammani ba, duwatsu suka ganka suka kaɗu domin tsoro.
4 Ba wanda ya taɓa gani ko jin labarin wani Allah kamarka, wanda ya yi waɗannan ayyuka ga waɗanda suka sa zuciyarsu gare shi.