11 “Ka roƙi Ubangiji Allahnka ya ba ka alama. Yana yiwuwa daga can zurfin lahira ne, ko kuma daga can cikin sama ne.”
12 Ahaz ya amsa, ya ce, “Ba zan nemi wata alama ba. Ba zan jarraba Ubangiji ba.”
13 Ga amsar da Ishaya ya ba Ahaz, “Kasa kunne yanzu, kai zuriyar sarki Dawuda. Ba abin kirki kuke yi ba, da kuka ƙure haƙurin jama'a, haƙurin Allah kuma kuke so ku ƙure?
14 Yanzu fa, Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel.
15 In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa.
16 Kafin lokacin ya yi, ƙasashen sarakunan nan biyu waɗanda suka firgita ku za su zama kango.
17 “Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama'arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Isra'ila daga na Yahuza. Zai kawo Sarkin Assuriya!