1 Da Adonizedek, Sarkin Urushalima, ya ji yadda Joshuwa ya ci Ai, har ya hallakar da ita sarai kamar yadda ya yi wa Yariko da sarkinta, da kuma yadda mazaunan Gibeyon suka yi amana da Isra'ilawa, har suna zama cikinsu.
2 sai ya tsorata ƙwarai, gama Gibeyon babban birni ce kamar ɗaya daga cikin alkaryai, har ma ta fi Ai girma, mazajenta duka kuwa ƙarfafa ne.
3 Adonizedek Sarkin Urushalima, ya aika zuwa ga Hoham Sarkin Hebron, da Firam Sarkin Yarmut, da Yafiya Sarkin Lakish, da Debir Sarkin Eglon, ya ce,
4 “Ku zo, ku taimake ni, mu yaƙi Gibeyon, gama ta yi amana da Joshuwa da Isra'ilawa.”
5 Sarakunan nan biyar na Amoriyawa, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon, suka tattaru da dukan rundunansu, suka haura, suka kafa wa Gibeyon sansani don su yaƙe ta.