27 Amma sa'ad da rana take faɗuwa, Joshuwa ya umarta, aka saukar da gawawwakinsu daga bisa itatuwan, aka jefa su cikin kogon inda suka ɓuya. Sa'an nan suka rufe bakin kogon da manyan duwatsu. Har wa yau suna nan.
28 A wannan rana kuwa Joshuwa ya ci Makkeda da yaƙi, ya kashe mutanenta da sarkinta da takobi, har ba wanda ya ragu. Ya yi wa Sarkin Makkeda kamar yadda ya yi wa Sarkin Yariko.
29 Joshuwa ya zarce, da shi da dukan Isra'ilawa zuwa Libna, suka yi yaƙi da Libna.
30 Ubangiji ya bashe ta da sarkinta a hannun Isra'ilawa, suka kuwa buge ta da takobi, da kowane mutum da yake cikinta, ba su rage kowa cikinta ba. Suka yi wa sarkinta kamar yadda suka yi wa Sarkin Yariko.
31 Joshuwa kuma ya zarce daga Libna, da shi da Isra'ilawa duka , zuwa Lakish, suka kewaye ta da yaƙi, suka auka mata.
32 Ubangiji ya ba da Lakish a hannun Isra'ilawa suka cinye ta da yaƙi cikin kwana biyu. Suka bugi kowane mutum da yake cikinta da takobi kamar yadda suka yi wa Libna.
33 Horam, Sarkin Gezer kuwa, ya kawo wa Lakish gudunmawa, Joshuwa kuwa ya buge shi tare da mutanensa, har ba wanda ya ragu.