40 Haka nan kuwa Joshuwa ya cinye dukan ƙasar tuddai, da Negeb, da filayen kwaruruka, da gangare, da sarakunansu duka, ba wanda ya ragu, amma ya hallaka su duka kamar yadda Ubangiji, Allah na Isra'ila ya umarta.
41 Joshuwa kuma ya cinye su da yaƙi tun daga Kadesh-barneya har zuwa Gaza, da dukan ƙasar Goshen har zuwa Gibeyon.
42 Joshuwa kuwa ya cinye sarakunan nan duka da ƙasashensu gaba ɗaya, gama Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi yaƙi domin Isra'ilawa.
43 Sa'an nan Joshuwa ya komo tare da dukan Isra'ilawa zuwa zango a Gilgal.