1 Yanzu Joshuwa ya tsufa ƙwarai, sai Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi, ƙasar da za ku mallaka ta ragu da yawa.
2 Wannan ita ce ƙasar da ta ragu, dukan ƙasar Filistiyawa, da ta Geshuriyawa,
3 daga Shihor da yake gabas da Masar zuwa iyakar Ekron a wajen arewa. Wannan ƙasa ta Kan'aniyawa ce. Akwai ƙasar sarakuna biyar na Filistiyawa da yake a Gaza, da Ashdod, da Ashkelon, da Gat, da Ekron, da ƙasar Awwiyawa,
4 da dukan ƙasar Kan'aniyawa a wajen kudu, da Meyara ta Sidoniyawa, zuwa Afek, har zuwa iyakar Amoriyawa,
5 da ƙasar Gebaliyawa, da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba'al-gad a gindin Dutsen Harmon zuwa iyakar Hamat,
6 da dukan mazaunan ƙasar tuddai, tun daga Lebanon zuwa Misrefot-mayim har da dukan Sidoniyawa. Ni da kaina zan kore su a gaban jama'ar Isra'ila. Kai kuwa za ka raba wa Isra'ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka.