17 da Heshbon, da dukan biranenta da suke kan tudu, wato Dibon, da Bamot-ba'al, da Ba'al-mayon,
18 da Yahaza, da Kedemot, da Mefayat,
19 da Kiriyatayim, da Sibma, da Zeret-shahar da yake bisa tudun da yake cikin kwarin,
20 da Bet-feyor, da gangaren Fisga, da Betyeshimot.
21 Waɗannan duka su ne birane na kan tudu, da dukan masarautar Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda ya sarauci Heshbon. Musa ya ci shi da yaƙi da shugabannin Madayana, wato Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba, wato sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar.
22 Jama'ar Isra'ila kuma suka kashe Bal'amu matsubbaci, ɗan Beyor, da takobi.
23 Urdun kuwa ya zama iyakar yankin ƙasar jama'ar Ra'ubainu. Wannan shi ne gādon Ra'ubainawa bisa ga iyalansu, da biranensu da ƙauyukansu.