5 Karkarar jama'ar Ifraimu, bisa ga iyalansu, ita ce iyakar gādonsu a wajen gabas, wato ita ce Atarot-addar har zuwa Bet-horon wadda take kan tudu.
6 Daga can iyakar ta miƙa zuwa teku ta bar Mikmetat a wajen arewa. A wajen gabas kuwa iyakar ta karkata zuwa Ta'anat-Shilo, daga can sai ta zarce gaba a wajen gabas zuwa Yanowa.
7 Daga Yanowa sai ta gangara zuwa Atarot da Nayaran, ta kuma gegi Yariko, sa'an nan ta gangara a Urdun.
8 Daga Taffuwa, sai iyakar ta yi yamma zuwa rafin Kana, sa'an nan ta gangara a teku. Wannan shi ne gādon Ifraimawa bisa ga iyalansu,
9 tare da garuruwan da ƙauyukan da aka keɓe wa Ifraimawa daga cikin gādon jama'ar Manassa.
10 Amma ba su kori Kan'aniyawa da suke zaune a Gezer ba, don haka Kan'aniyawa ka zauna tare da Ifraimawa har wa yau, amma Kan'aniyawa suka zama bayi masu yin aikin dole.