1 Kuri'a ta biyu ta faɗa kan kabilar Saminu bisa ga iyalanta. Nasu rabon gādon yana tsakiyar rabon gādon kabilar Yahuza.
2 Waɗannan su ne wuraren da suka gāda, Biyer-sheba, da Sheba, da Molada,
3 da Hazar-shuwal, da Bilha, da Ezem,
4 da Eltola, da Betul, da Horma,
5 da Ziklag, da Bet-markabot, da Hazar-susa,
6 da Bet-lebawot, da Sharuhen. Garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu.