19 da Hafarayim, da Shiyon, da Anaharat,
20 da Rabbit, da Kishiyon, da Ebez,
21 da Remet da En-ganim, da En-hadda, da Bet-fazzez.
22 Iyakar kuma ta bi ta Tabor, da Shahazuma, da Bet-shemesh. Sa'an nan ta gangara a Kogin Urdun. Akwai garuruwa goma sha shida da ƙauyukansu.
23 Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke a yankin ƙasar da kabilar Issaka ta gāda bisa ga iyalanta.
24 Kuri'a ta biyar ta fāɗo a kan kabilar Ashiru bisa ga iyalanta.
25 Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar, su ne Helkat, da Hali, da Beten, da Akshaf,