32 Kuri'a ta shida ta faɗo a kan kabilar Naftali bisa ga iyalanta.
33 Tasu iyaka, ta miƙa daga Helef, daga itacen oak da yake cikin Za'anannim, da Adami-nekeb, da Yabneyel har zuwa Lakkum, sa'an nan ta tsaya a Kogin Urdun.
34 Iyakar kuma ta juya wajen kudu zuwa Aznot-tabor, daga can ta miƙa zuwa Hukkok, sa'an nan ta kai Zabaluna wajen kudu, da Ashiru wajen yamma, da Yahuza wajen gabas wajen Urdun.
35 Garuruwan da yake da garu su ne, Ziddim, da Zer, da Hammat, da Rakkat, da Kinneret,
36 da Adama, da Rama, da Hazor,
37 da Kedesh, da Edirai, da En-hazor,
38 da Iron, da Migdal-el, da Horem, da Bet-anat, da Bet-shemesh. Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu.