1 Sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa,
2 “Ka faɗa wa jama'ar Isra'ila, su keɓe biranen mafaka waɗanda na faɗa wa Musa ya faɗa muku.
3 Domin idan wani mutum ya yi kisankai ba da niyya ba, ba kuma da saninsa ba, sai ya tsere zuwa can. Biranen za su zama muku mafaka daga mai bin hakkin jini.
4 Wanda ya yi kisankan sai ya tsere zuwa ɗaya daga cikin biranen, ya tsaya a bakin ƙofar birnin, ya bayyana wa dattawan garin abin da ya same shi. In sun ji, sai su shigar da shi a birnin, su ba shi wurin zama, ya zauna tare da su.