10 Sa'ad da suka kai Gelilot, kusa da Urdun, a gefen da yake wajen ƙasar Kan'ana, suka gina babban bagade a wurin.
11 Sauran Isra'ilawa kuwa suka ji labari cewa, “Ga shi, Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa sun gina bagade a Gelilot a kan iyakar ƙasar Kan'ana, a wajen hayinsu na yammacin Urdun.”
12 Da Isra'ilawa suka ji haka sai dukansu suka tattaru a Shilo don su kai musu yaƙi.
13 Mutanen Isra'ila kuwa suka aiki Finehas, ɗan Ele'azara, firist, wurin Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad.
14 Shugabanni goma suka tafi tare da shi, shugaba ɗaya daga kowace kabilar Isra'ila. Kowane ɗayansu shugaba ne a danginsa a kabilar Isra'ila.
15 Da suka zo wurin Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad, ya ce musu,
16 “In ji dukan taron jama'ar Ubangiji, ‘Wane irin cin amana ne wannan da kuka yi wa Allah na Isra'ila har da kuka bar bin Ubangiji yau?’ Kun tayar wa Ubangiji yau da kuka gina wa kanku bagade.