5 Na aiki Musa da Haruna, na aukar wa Masar da annobai ta wurin abin da na yi a cikinta daga baya kuma na fisshe ku.
6 Na kuwa fitar da kakanninku daga Masar. Da suka zo Bahar Maliya, sai Masarawa suka fafari kakanninku da karusai da mahayan dawakai har zuwa teku.
7 A sa'ad da suka yi mini kuka, na sa duhu a tsakaninsu da Masarawa, na sa teku ta shafe Masarawa. Da idonku kun ga abin da na yi wa Masar, kuka kuma zauna a jeji da daɗewa.
8 Sa'an nan na kawo ku a ƙasar Amoriyawa, waɗanda suka zauna a wancan hayin Urdun, waɗanda kuma suka yi yaƙi da ku, na kuwa ba da su gare ku, na hallaka su, kuka mallaki ƙasarsu.
9 Haka kuma Balak, ɗan Ziffor, Sarkin Mowab, ya tashi ya yi yaƙi da Isra'ila, har ya gayyaci Bal'amu, ɗan Beyor, ya zo ya la'anta ku.
10 Amma ban saurari Bal'amu ba, saboda haka ya sa muku albarka, ta haka na cece ku daga hannunsa.
11 Da kuka haye Urdun, kuka zo Yariko, mutanen Yariko kuwa suka yi yaƙi da ku, haka kuma Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Kan'aniyawa da Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, amma na ba da su a gare ku.