1 Da al'umma duka suka gama haye Urdun, sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa,
2 “Ɗauki mutum goma sha biyu daga cikin jama'a, wato mutum ɗaya na kowace kabila.
3 Ka umarce su su ɗauki duwatsu goma sha biyu daga tsakiyar Urdun daidai inda firistoci suka tsaya, su haye da su, su ajiye su a masaukin da za su kwana yau.”
4 Sai Joshuwa ya kirawo mutum goma sha biyu waɗanda ya zaɓa daga cikin Isra'ilawa, mutum guda na kowace kabila.