1 Sa'ad da dukan sarakunan Amoriyawa waɗanda suke wannan hayi, wato yamma da Urdun, da dukan sarakunan Kan'aniyawa da suke bakin teku, suka ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Urdun ya ƙafe don Isra'ilawa, har suka haye, sai zukatansu suka narke, har ba wanda yake da sauran kurwa a cikinsu saboda tsoron Isra'ilawa.
2 A lokacin kuwa Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Ka yi wuƙaƙe na duwatsu, ka yi wa mazajen Isra'ila kaciya.”
3 Sai Joshuwa ya yi wuƙaƙe na duwatsu, ya yi wa mutanen kaciya a Gibeyat-ha'aralot, wato dutsen kaciya.
4-5 Dalilin da ya sa Joshuwa ya yi musu kaciya ke nan, domin dukan waɗanda aka haifa a hanya cikin jeji bayan fitowarsu daga Masar, ba a yi musu kaciya ba. Dukan mazajen da suka fito daga Masar waɗanda suka isa yaƙi sun rasu cikin jeji a hanyarsu. Waɗannan kuwa an yi musu kaciya kafin fitowarsu.