1 Aka rufe Yariko ciki da waje, ba mai fita, ba mai shiga saboda Isra'ilawa.
2 Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Duba, na ba da Yariko, da sarkinta, da jarumawanta a hannunka.
3 Kai da dukan mayaƙa za ku zagaya birnin sau ɗaya kowace rana har kwana shida.
4 Sai firistoci bakwai su riƙe ƙahonin raguna a gaban akwatin alkawari. Amma a rana ta bakwai za ku zaga birnin sau bakwai, firistoci su yi ta busar ƙahoni.
5 Sa'ad da suka tsawaita busar ƙahoni, sai dukan jama'a su yi ihu da babbar murya, garun birnin kuwa zai rushe tun daga tushensa. Sai mutane su haura, ko wanne ya nufi inda ya fuskanta sosai zuwa cikin birnin.”