6 don su fahimci ɓoyayyiyar ma'anar da take cikin karin magana, da mawuyatan al'amura waɗanda masu hikima suka ƙago.
7 In kana so ilimi dole ne ka fara da tsoron Ubangiji. Jahilai ba su san darajar hikima ba, sun kuwa ƙi su koya.
8 Ɗana, ka kasa kunne ga koyarwar mahaifinka, ka mai da hankali ga abin da mahaifiyarka take faɗa.
9 Koyarwarsu za ta inganta halinka, ta zama kayan ado kamar kyakkyawan rawani a kanka, ko kyakkyawan abin wuya a wuyanka, don su ƙara maka kyau.
10 Ɗana sa'ad da masu zunubi suka jarabce ka, kada ka yarda
11 in suka ce maka, “Zo mu tafi mu nemi wani mutum mu kashe, mu je, mu fāɗa wa marasa laifi mu ji daɗi!
12 Ba mu damu da ransu da lafiyarsu ba, mu dai mu tafi mu kashe su, mu hallaka su ɗungum.