12 Hasalar sarki kamar rurin zaki ne, amma alherinsa kamar saukar ruwan sama ne.
13 Dakikin ɗa yana jawo wa mahaifinsa lalacewa, mace mai mita tana kama da ɗiɗɗigar ruwa.
14 Mutum na iya cin gādon gida da kuɗi daga wurin iyayensa, amma Ubangiji ne kaɗai yake ba shi mace mai hankali.
15 Rago, yi ta ragwancinka ka yi ta sharar barci, amma kai za ka sha yunwa.
16 Ka kiyaye umarnai za ka rayu, in ka ƙi binsu kuwa za ka mutu.
17 Sa'ad da ka bayar ga matalauci kamar ka ba Ubangiji rance ne, gama Ubangiji zai sāka maka.
18 Ka yi wa 'ya'yanka tarbiyya tun suna ƙanana yadda za su iya koyo. Idan ba ka yi haka ba, ka taimaka wajen lalacewarsu ke nan.