12 Adali ya san tunanin mugaye, yakan kuwa zama sanadin lalacewarsu.
13 Idan ka ƙi jin kukan matalauci, naka kukan da kake yi na neman taimako, ba za a ji ba.
14 Kyauta a asirce takan kwantar da zuciyar wanda yake fushi da kai.
15 Sa'ad da aka yi adalci mutanen kirki sukan yi murna, amma mugaye sukan yi baƙin ciki.
16 Mutuwa tana jiran wanda ya ƙi bin hanyar hankali.
17 Sa kai cikin nishaɗi, wato shan ruwan inabi, da cin abinci mai tsada, ba zai bar ka ka tara dukiya ba.
18 Wahalar da mugaye suke so su jawo wa mutanen kirki, za ta koma kansu.