18-19 Mutum wanda yakan ruɗi maƙwabcinsa sa'an nan ya ce, wasa yake yi kawai, yana kama da mahaukaci wanda yake wasa da wuta, da kibau, da mutuwa.
20 Idan ba itace wuta takan mutu, haka kuma idan ba mai gulma ba za a yi jayayya ba.
21 Kamar yadda gawayi yake ga garwashin wuta, itace kuma ga wuta, haka mai gardama yake ga jayayya.
22 Kamar yadda lomar abinci mai daɗi takan gangara can cikin ciki haka maganar mai gulma take.
23 Bakin da ba ya faɗar gaskiya, da zuciya mai ƙiyayya suna kama da kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba.
24 Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye ta da maganar bakinsa, yana kuma ƙunshe da munafunci.
25 Sa'ad da yake magana mai kyau kada ka gaskata shi, domin zuciyarsa tana cike da mugunta.