18 Inda ba a bin faɗar Allah, jama'a za su kangare, amma mai farin ciki ne wanda yake kiyaye dokar Allah.
19 Bara ba ya horuwa ta wurin magana kawai, gama ko da ya fahimta ma, ba zai kula ba.
20 Ka ga mutum mai garajen yin magana? To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi.
21 Baran da aka shagwaɓa tun yana yaro, a ƙarshe zai ɗauki kansa tankar magājin gida.
22 Mutum mai saurin fushi yakan ta da faɗa, mai zafin rai kuma yakan aikata laifi da yawa.
23 Girmankan mutum zai jawo masa ƙasƙanci, amma za a girmama mai tawali'u.
24 Abokin ɓarawo mugun maƙiyin kansa ne, yana jinsa yana ta rantsuwa, amma ba zai ce kome ba.