1 'Ya'yan Haruna, maza, Nadab da Abihu kuwa kowannensu ya ɗauki faranti ya sa wuta, ya zuba turare a kai, ya miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba.
2 Sai wuta ta fito daga wurin Ubangiji ta kashe su, suka mutu a gaban Ubangiji.
3 Musa kuwa ya ce wa Haruna, “Wannan ita ce ma'anar abin da Ubangiji yake cewa, ‘Dukan waɗanda suke bauta mini, dole su nuna ladabi ga tsarkina, zan kuma bayyana ɗaukakata ga jama'ata.’ ” Haruna kuwa ya yi tsit.
4 Musa ya kirawo Mishayel da Elzafan 'ya'ya maza na Uzziyel, kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan, ku ɗauki gawawwakin 'yan'uwanku daga gaban wuri mai tsarki zuwa bayan zango.”