4 Musa ya kirawo Mishayel da Elzafan 'ya'ya maza na Uzziyel, kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan, ku ɗauki gawawwakin 'yan'uwanku daga gaban wuri mai tsarki zuwa bayan zango.”
5 Sai suka zo, suka kama rigunan matattun suka ɗauke su zuwa bayan zango kamar yadda Musa ya faɗa.
6 Musa kuma ya ce wa Haruna, da 'ya'yansa maza, wato, Ele'azara da Itamar, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku kyakketa rigunanku don kada ku mutu, don kada Ubangiji ya yi fushi da taron jama'a duka, amma 'yan'uwanku, wato, dukan Isra'ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya ƙone.
7 Kada kuwa ku fita daga cikin alfarwa ta sujada don kada ku mutu, gama an shafa muku man keɓewa na Ubangiji.” Sai suka yi yadda Musa ya faɗa.
8 Ubangiji kuma ya yi magana da Haruna ya ce,
9 “Kada kai da 'ya'yanka maza ku sha ruwan inabi, ko abin sha mai ƙarfi sa'ad da za ku shiga alfarwa ta sujada don kada ku mutu. Wannan doka ce a dukan zamananku.
10 Sai ku bambanta tsakanin abu mai tsarki da marar tsarki, da tsakanin abin da yake halal da abin da yake haram.