55 Firist kuma zai sāke duban abin da yake da cutar bayan da aka wanke shi, idan ya ga launin cutar bai sāke ba, ko da cutar ba ta yaɗu ba, abin ya zama marar tsarki ne nan, sai a ƙone shi da wuta, ko tabon cutar yana cikin abin ne, ko a waje.
56 Amma idan firist ɗin ya duba ya ga tabon ya dushe bayan da aka wanke shi, sai ya kece wurin daga fatar, ko tariyar zaren, ko waɗarin.
57 Idan tabon ya sāke bayyana kuma a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, ya yaɗu, sai a ƙone abin da yake da kuturtar.
58 Amma da rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko kowane abin da aka yi da fata, wanda cutar ta wanku daga shi sa'ad da aka wanke, sai a sāke wanke shi, ya kuwa zama tsarkakakke ke nan.
59 Wannan ita ce dokar da za a bi a kan cutar kuturtar rigar ulu ko ta lilin, ko cutar kuturta ta tariyar zaren, ko ta waɗarin, ko kuma ta kan kowane abu da aka yi da fata, don a tabbatar tsattsarka ne, ko marar tsarki ne.