1 Ubangiji ya ba Musa
2 waɗannan ka'idodi da za a bi a ranar tsarkakewar mai kuturta. Sai a kawo shi ga firist.
3 Firist ɗin zai fita zuwa bayan zango ya dudduba shi. Idan kuturun ya warke daga cutar kuturtar,
4 firist ɗin zai umarta a kawo tsuntsaye biyu masu rai, masu tsabta, da itacen al'ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya domin aikin tsarkakewa.
5 Sai firist ya umarta a yanka tsuntsu ɗaya a kaskon da yake cike da ruwa mai gudu.
6 Ya kuma ɗauki ɗayan tsuntsu, da itacen al'ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya, ya tsoma su cikin jinin tsuntsun da aka yanka a ruwan kaskon.
7 Sai ya yayyafa jinin sau bakwai a kan wanda za a tsarkake daga kuturtar, sa'an nan ya hurta, cewa, mutumin ya tsarkaka, ya kuma saki tsuntsu mai ran ya tafi cikin saura.