22 Haka kuma duk wanda ya taɓa kowane abin da ta zauna a kai, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.
23 Ko gado ne, ko kuma kowane abin da ta zauna a kai, sa'ad da wani ya taɓa shi zai ƙazantu har maraice.
24 Idan kuma wani ya kwana da ita, rashin tsarkinta zai shafe shi. Zai zama marar tsarki har kwana bakwai. Kowane gado da ya kwanta a kai zai ƙazantu.
25 Idan zubar jinin hailar macen ya yi kwanaki da yawa, ko kuwa kwanakin hailarta sun zarce ka'ida, a duk kwanakin zubar jininta za ta lizima cikin rashin tsarki daidai kamar lokacin hailarta.
26 Kowane gado da ta kwanta a kai a kwanakin zubar jininta, zai zama ƙazantacce, daidai kamar lokacin hailarta. Kowane abin da ta zauna a kai zai ƙazantu kamar a lokacin hailarta.
27 Wanda duk ya taɓa waɗannan abubuwa zai ƙazantu, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.
28 Bayan da hailarta ta tsaya, za ta ƙidaya kwanaki bakwai, bayan haka za ta tsarkaka.