30 Firist ɗin zai miƙa ɗaya hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda rashin tsarkinta.
31 Ta haka za ka tsarkake jama'ar Isra'ila daga rashin tsarkinsu, domin kada su mutu saboda rashin tsarkinsu ta wurin ƙazantar da alfarwata wadda take tsakiyarsu.
32 Waɗannan su ne ka'idodi a kan wanda yake ɗiga, da wanda yake zubar da maniyyi, ƙazantacce ne.
33 Haka kuma wadda take haila, da kowane namiji ko mace, da yake ɗiga, da namijin da ya kwana da mace marar tsarki.