4 bai kuwa kawo shi a ƙofar alfarwa ta sujada don ya miƙa shi sadaka ga Ubangiji a gaban alfarwa ta sujada ba, alhakin jinin da ya zubar yana bisa kansa, za a fitar da wannan mutum daga cikin jama'arsa.
5 Manufar wannan umarni ce domin Isra'ilawa su riƙa kawo hadayunsu, waɗanda sukan yi a filin saura ga Ubangiji a wurin firist a ƙofar alfarwa ta sujada. Sai su yanka hadayu na salama ga Ubangiji.
6 Sai firist ya yayyafa jinin a kan bagaden Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada. Zai ƙone kitsen don ya ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.
7 Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan doka ce ta har abada a gare su har dukan zamanansu.
8 Kowane Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu, wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ko sadaka,
9 amma bai kawo ta a ƙofar alfarwa ta sujada, ya miƙa ta ga Ubangiji ba, sai a fitar da wannan mutum daga cikin jama'a.
10 Idan wani Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu ya ci jini, Ubangiji zai yi gāba da wannan mutum da ya ci jinin ya fitar da shi daga cikin jama'a.